in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutane a Afirka zai kai kashi 40 cikin dari na dukkan al'ummar duniya a karshen karnin nan, in ji MDD
2014-08-21 10:33:56 cri
Wani rahoton da asusun kula da yara na MDD Unicef ya baya baya-bayan nan ya yi hasashen cewa, kasancewar nahiyar Afirka mafi samun karuwar yawan al'umma, yawan jirajiran da za a haifa daga shekarar 2015 zuwa 2050 a nahiyar zai kai biliyan 1.8, yayin da yawan mutane a nahiyar zai karu daga biliyan 1 zuwa biliyan 2. Kuma ya zuwa karshen wannan karnin, yawan mutane a nahiyar Afirka zai kai biliyan 4, wanda zai kai kashi 40 cikin dari na dukkan al'ummar duniya.

Yankunan da ke gabashi da yammacin Afirka yankuna ne da aka fi samun yawan al'umma a nahiyar, inda ake hasashen samun kaso biyu bisa uku na daukacin yawan al'ummar Afirka a wannan yanki nan da shekarar 2050.

Kasar Nijeriya kuwa kasa ce da aka fi samun yawan haihuwa a nahiyar Afirka, inda ake sa ran samun kashi 20 cikin dari na daukacin yawan jirajiran Afirka a kasar nan da shekarar 2015, yayin da wannan jimilla za ta kai kashi 10 cikin dari na dukkan yawan jirajiran duniya nan da shekarar 2050. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China