in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gabatar da rahoton MDD game da zuba jari a Afirka
2014-09-10 16:02:49 cri
Hukumar raya masana'antu ta MDD ta UNIDO ta gabatar da wani rahoto game da zuba jari a Afirka na shekarar 2013. Wannan ne dai karon farko da MDDr ta gabatar a irin wannan rahoto a nan kasar Sin, an kuma gabatar da shi ne a ranar 9 ga watan nan a birnin Xiamen.

Rahoton ya nuna cewa kafin shekarar 2013, jarin da kasashen waje suka zuba a nahiyar Afirka ya yi kasa da yawan GDPn nahiyar da kashi 15 cikin dari.

Shugaban sashen kula da harkokin cinikayya, da zuba jari da fasahohi na UNIDO Mr. Lamine Dhaoui, ya bayyana cewa, MDD tana fatan za a kafa wani dandali na sa ido na yanki, don sa kaimi ga zuba jari ga kasashen nahiyar ta Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China