Sharhin ya ce, a 'yan kwanakin baya, an kai jerin hare-haren ta'addanci masu muni a wasu sassa na kasar Sin, wadanda ba a iya raba su da manufofin tsattsauran ra'ayin addini.
Jaridar ta ce tsattsauran ra'ayin addini ya murde ka'idojin addini kan yunkurin neman kawo wa kasa baraka, da kuma rura wutar rikici da 'yan ta'adda ke burin aiwatarwa.
Haka zalika, sharhin da jaridar ta yi ya nuna cewa lallai ba za a iya samun jituwa a tsakanin addinai daban daban, da hadin kan kabilu mabanbanta, da kuma zaman karko a zamantakewar al'umma ba, har sai an yi biyayya ga ka'idoji na "ba da kariya ga lamuran halal, da hana haramtattun abubuwa, da shawo kan masu tsattsauran ra'ayi, da tasirin kutsa kai da sassan ketare ke yi wa kasar Sin, baya ga yaki da laiffuffuka", ta yadda jama'a kimanin miliyan 22 da ke jihar Xinjiang za su iya samun zaman lafiya mai dorewa.
Bugu da kari, sharhin ya nanata cewa, biyan halastattun bukatun masu bin addini, da horar da limamai masu kishin kasa, muhimman ayyuka ne na gudanar da ayyukan addini yadda ya kamata.(Kande Gao)