Babban sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya nuna yabo a ranar Asabar kan shawarwarin siyasa na matsayin koli da aka yi tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu a yayin bikin rufe wasannin Asiya na Incheon.
Kamar yadda sakatare janar yake ci gaba da maimaitawa, yin shawarwari ita ce manufa guda ta warware manyan batutuwa, in ji kakakin Ban Ki-moon a cikin wata sanarwa. Akwai abun kwarin gwiwa ga yadda bangarorin biyu suka amince wajen shirya wani sabon zagayen shawarwarin matsayin koli cikin gaggawa, in ji sanarwar.
A cikin sanarwar, sakatare janar na MDD ya jaddada fatansa na ganin bangarorin biyu da abin ya shafa sun ci gaba da yunkuri da zai kai yankin Koriya cikin zaman lafiya kuma inda babu makaman nukuliya.
Manyan jami'an Koriya ta Arewa uku, Hwang Pyong So, Choe Ryong Hae da Kim Yang Gon sun isa a ranar Asabar a filin jirgin saman kasa da kasa na Incheon, domin halartar bikin rufe wasannin Asiya.
Manyan jami'an uku sun samu tattaunawa tare da takwarorinsu na kasar Koriya ta Kudu, inda a cikinsu akwai babban mashawarci a fuskar tsaro na fadar shugaban kasar, Kim Kwan-jin da kuma ministan kula da harkokin dunkulewar kasar Ryoo Kihl-jae. (Maman Ada)