in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nanata matsayinta na ganin an kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya
2013-12-18 19:32:35 cri
Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta na ganin an kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da daidaita matsala ta hanyar yin shawarwari tsakaninsu, sannan matsayin kasar Sin game da nukuliyar kasar Koriya ta Arewa a fili yake, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Hua Chunying ta sanar a yau Laraba 18 ga wata a nan birnin Beijing.

A jiya 17 ga wata, jaridar Rodong Simun ta Koriya ta Arewa ta gabatar da sharhin edita da ke cewa, kasar ta fara mallakar makaman nukiliya ne bisa kokarin marigayi Kim Jong Il.

Game da wannan batu, madam Hua ta nanata matsayin Sin a gun taron 'yan jarida da aka shirya a yau cewa, Sin tana tsayawa kan matsayinta na ganin an kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin, tare da kokarin daidaita matsala ta hanyar yin shawarwari tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China