Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi bayani kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Koriya ta Arewa
A ranar Laraba 17 ga wata, game da tambayar cewa, yanzu kwamitin sulhu na MDD ya kakaba takunkumi kan kasar Koriya ta Arewa, sannan kuma ana ganin cewa, a kwanakin baya kasar Sin ta taba bayyana cewa, za ta tabbatar da dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Koriya ta Arewa yadda ya kamata, yanzu yaya wannan shiri yake ga Sin?
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying ta yi bayanin a taron manema labarai da aka saba yi kullum a nan birnin Beijing cewa, kwamitin sulhu na MDD ya riga ya yanke shawara bisa matakinta kan abin da yake gabanta, kuma kasar Sin a matsayinta na zaunanniyar mamba ta kwamitin sulhu, kuma daya daga cikin kasashen duniya masu sauke nauyin dake kanta, za ta bi kudurorin MDD., tare da daukar nauyinta yadda ya kamata.(Fatima)