Sin ta nuna rashin jin dadi kan sake farfado da tasoshin nukiliya na Koriya ta Arewa
A ranar Talata 2 ga wata, game da batun sake farfado da tasoshin mukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta yi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, Sin ta nuna rashin jin dadi kan wannan batu, don haka take kira ga bangarori daban daban da su yi hakuri, a kokarin komawa hanyar yin shawarwari tsakaninsu cikin sauri.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Koriya ta Arewa KCNA ya bayar a ranar 2 ga wata, mai magana da yawun babbar hukumar makamashin nukiliya ta kasar ya bayyana a ranar cewa, kasar za ta sake farfado da tasoshin nukiliya dake yankin Yongbyon.(Fatima)