in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin aikin gona na kasashen BRICS sun tattauna batun ingancin abinci
2013-10-30 15:01:53 cri

An fara taron ministocin aikin gona karo na uku na kasashe da tattalin arzikinsu ke bunkasa,wato Brazil,Rasha,Indiya,Sin da Afirka ta kudu(BRICS) a ran Talata 29 ga wata a birnin Pretoria, fadar gwamnatin kasar Afirka ta kudu ,inda za su tattauna kan yadda za a kawar da illar da matsalar sauyin yanayin duniya ta yiwa kokarin da ake yi na samar da abinci a duniya yadda ya kamata.

A wannan rana, bangarori daban daban da suka halarci taron sun daddale wata hadaddiyar sanarwa, wadda ta ce, wadannan kasashe 5 za su hada kai a bangaren aikin gona da yankunan karkara bisa moriyar juna, zurfafa tattaunawa kan samar da dabarun da za su taimaka wajen tinkarar kalubaloli da ake fuskanta.

Ministan aikin gona na kasar Sin Mista Han Changbin ya bayyana a gun taron cewa, hadin kan kasashen BRICS a bangaren aikin gona zai yi kyakkyawan tasiri wajen daidaita matsalolin samar da abinci yadda ya kamata a duniya da matsalar sauyin yanayin duniya. Kasar Sin ta yi fatan cewa, ta hanyar hada kai da sauran kasashen BRICS, za ta iya sa kaimi ga bunkasuwar aikin gona da samar da abinci yadda ya kamata a duniya. Don haka sai ya yi kira ga kasashen BRICS da su dauki matakai don su kara taka rawa wajen rage kalubalolin da matsalar sauyin yanayi ke yi wa aikin gona, da sa kaimi ga raya aikin gona cikin dogon lokaci, da tabbatar da samar da abinci yadda ya kamata a duniya.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China