Babbar daraktar hukumar UNESCO Irina Bokova ta shedawa manema labaru a cibiyar MDD dake birnin New York cewa, Sin ta baiwa hukumarta taimako a fannoni daban-daban, kana tana alfahari sosai da gudunmawar da Sin take bayar ta fuskar sa kaimi ga al'adu, ba da ilmi, kimiya da dai sauransu.
Kazalika, babbar daraktar ta ce, ban da sa kaimi ga mu'ammalar al'adu, kuma Sin ta yi kokari sosai wajen goyon bayan sha'anin ba da ilmi a Afrika. Yanzu, Sin da UNESCO suna gudanar da hadin kai ta fuskar horar da malaman Afrika. Ta ce tana farin ciki sosai da Sin za ta ci gaba da tallafawa hukumar kan wannan aiki, abin da zai taimakawa wadansu kasashe mafi koma baya a Afrika wajen samun ilmi. (Amina)