Hukumar gudanarwar UNESCO wata babbar hukuma ce mai kunshe da mambobi 58, wadanda ake zaba yayin babban taron hukumar, sa'annan wa'adin aikin ko wace mambarta ke kasancewa shekaru hurhudu. Haka nan bayan ko wane shekaru biyu a kan zabi rabin mambobin hukumar. A zaman babban taron da aka yi ran 13 ga wata, gaba daya mambobin kasashe 28, sun cimma nasarar zama mambobin hukumar, tare da sauran mambobi guda 30 da aka zaba a shekarar 2011, jimillar mambobin da za su kasance sabuwar hukumar gudanarwa ta UNESCO.
Bisa ka'idojin hukumar ta UNESCO, ana zabar mambobin hukumar bisa yankuna daban daban, watau kasar Sin tana yankin Asiya da Pasifik, mai kunshe da 'yan takara 7, a zaben na wannan karo kasar Sin ta kasance ta farko wajen samun kari'u, lamarin ya sa za ta ci gaba da zama mambar hukumar. (Maryam)