Taron shiyya na kwararrrun hukumar kula da ayyukan ba da ilmi da kimiyya da kuma al'adu UNESCO na fadakarwa kan sauyin yanayi domin samun cigaba mai karko da karbuwa a Afrika zai gudana a Mauritius a yau ranar Laraba. Dandalin na kwanaki uku zai tattara kimanin wakilai dari daga yankunan gabashin Afrika, kuriyar Afrika da tekun Indiya, kuma zaman taron zai mai da hankali kan kalubale da sauyin yanayi ke iyar kawowa ga tsare-tsaren ilimantarwa a Afrika da matsayin da ilmi zai kawo ga karbuwa da rage kaifin sauyin yanayi. Mahalarta taron za su bullo da tsarin aiki na bunkasa ba da ilmi a matsayin wani muhimmin makami wajen kyautata karbuwar sauye-sauyen yanayi bisa manufar samun cigaba mai karko a kasashen Afrika. (Maman Ada)