Liu Yandong ta ce, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai game da hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da hukumar UNESCO, kuma tana fatan ci gaba da fadada hadin gwiwa a tsakaninsu, da kara cusa abubuwa cikin hadin gwiwa a tsakaninsu ta hanyoyi da dama, don kara inganta mu'amalar al'adu a tsakanin kasashe da dama, don ba da gudummawa wajen samun dauwamammen ci gaba na dan Adam.
A nata bangare kuma, Bokova ta jinjina dangantakar hadin gwiwa a tsakanin bangarori biyu, kuma tana fatan inganta hadin gwiwa a fannin ilmi da kimiyya da al'adu a tsakaninsu.(Bako)