A cikin wata sanarwa da aka fitar a Paris babban birnin kasar Faransa,ofishin kula da ilimi,kimiyya da al'adu UNESCO yace malamin Turanci shine matakin farko da za'a dauka a kimiyyar wayar salula domin inganta yanayin koyarwa ga malaman makarantun firamare,inji Steven Vosloo Jami'in na UNESCO.
Mr Vosloo yace manufar shirin tun farko shi ne a samar da wani taimakon da malaman dake fuskantar wani mawuyacin hali kuma ba wani kafar samun taimako za su iya samu cikin sauri. Yana mai nuni da cewa kimiyyar wayar salula wata kafa ce tabbatacce kuma a wassu lokuta hanyar data fi dacewa a bangaren fasasha.
Kowa na iya mallaka a Nigeriya a inda kusan kowane dan kasa na amfani da wata kafar sadarwar wayar salula,wannan shirin zai aika da sakonni na mussaman domin malamai da sakonnin shawarwari a duk rana. Ya ce wannan shirin zai cimma dubban malaman makarantu a fadin kasar, inda kusan kashi 42 cikin dari ko kuma ace miliyan 10 da wani abu na yara dai dai karatun firamare basu iya zuwa makaranta, sannan yaran da suka samu zuwa makarantar suna kokarin ganin sun koyi gwargwadon ilimin yaki da jahilci da lissafi.
Shi dai irin wannan shirin na bullo da salon kayar da malaman makarantu ta amfani da kimiyyar wayar salula an riga an fara amfani da shi a kasashen Mozambique,P akistan,Afirka ta Kudu,Nijar,Kenya da kuma Mangoliya inda tsarin su ya bayar da kafar samun ilimi daga nesa wanda kuma ya inganta ilimin musamman a tsakanin mata da manyan mata,inji Jami'in na UNESCO. (Fatimah Jibril)