in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNESCO ta sanya cibiyar kayan tarihi dake Agadez cikin jerin muhimman ababen tarihi na duniya
2013-06-23 16:09:38 cri

Taron kwamitin kula da kayan tarihi karo na 37 dake gudana karkashin hukumar UNESCO a birnin Phnom Penh na kasar Cambodiya, ya amince da sanya cibiyar adana kayan tarihi dake birnin Agadez a Jamhuriyar Nijar, cikin muhimman kayayyakin tarihi na duniya. Matakin da ya sanya wannan cibiya shiga jerin wurare 3 a kasar ta Nijar da suka samu shiga wannan jadawali.

Wani kundi dake kunshe da bayanai kan wannan batu na majalissa mai lura da kayayyaki da wuraren tarihi karkashin hukumar ta UNESCO da ake wa lakabi da ICOMOS, ya bayyana wannan cibiya dake Agadez, a matsayin wadda ta shahara matuka, wadda kuma ke da dadadden tarihi dake komawa ga karni na 15, ta kuma kunshi manyan gine-ginen gidaje, da masallatai masu dogwayen hasumiyoyi, da kuma fadojin sarakuna ginin kasa irin na gargajiya.

Har ila yau kundin bayanan ya bayyana babbar hasumiyar dake cibiyar mai tsahon mita 27, a matsayin mafi tsayi a dukkanin fadin duniyar nan, da aka gina dukkanin sassanta da kasa.

Mataimakin shugaban taron kwamitin kula da kayan tarihin karo na 37 Francisco Javier Gutierrez, ya taya jamhuriyar ta Nijar murnar samun wannan nasara, jim kadan da bayyana sunan wannan cibiya tata cikin jerin manyan kayayyakin tarihin na duniya. Za dai a karkare taron na bana ne a yankin Angkor ranar 27 ga watan nan da muke ciki, inda kafin kammala shi ake sa ran sanya ababen tarihi 17 cikin 30 da aka mika sunayensu, cikin jadawalin muhimman kayayyakin tarihin na hukumar ta UNESCO.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China