in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci a tallafawa kasashen da suka sha fama da tashin hankali
2014-03-27 10:49:44 cri

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa kasashen da suka sha fama da rigingimu, wajen magance musabbabin fadawarsu cikin rikici. Ciki hadda batun magance matsalolin tattalin arziki da na zamantakewar al'ummun kasashen.

Mr. Liu ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci gaban mahalarta babban zaman MDD, don gane da ayyukan hukumar wanzar da zaman lafiya ta PBC a jiya Laraba. Ya ce, koma baya a fannin tattalin arziki da zamantakewa ne musabbabin rikice-rikicen dake addabar kasashe da dama.

Don haka ya yi kira ga kasashen duniya, da su mai da hankali ga batun samar da kudade, da dabarun tallafawa irin wadancan kasashe wajen gaggauta farfadowarsu.

Har ila yau manzon na kasar Sin, ya bayyana cewa, kasashen da suka sha fama da rikice-rikicen ne ke da nauyin warware matsolinsu a matakin farko, duba da banbance-banbance, ta fuskar tarihi da al'adu tsakanin kasashe mabanbanta. Yayin da a hannu guda ragowar kasashe ya dace, su martaba ra'ayi, da ikon irin wadannan kasashe a yunkurin suna farfadowa.

Daga nan sai ya nanata muhimmancin hadin gwiwar MDD, da hukumomi irin PBC, a fagen aiwatar da managartan manufofin wanzar da zaman lafiya mai dorewa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China