in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin wanzar da zaman lafiya ya samu cikakkiyar nasara a Saliyo
2014-03-27 10:41:23 cri

Yayin da ake gaf da kammala shirin wanzar da zaman lafiya, wanda ofishin MDD na UNIPSIL ya jagoranta a kasar Saliyo, shugaban ofishin Jens Anders Toyberg-Frandzen, ya ce, shirin ya cimma nasara maras iyaka.

Toyberg-Frandzen ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin da yake fayyacewa zauren kwamitin tsaron MDD ayyukan da ofishin na UNIPSIL ya gudanar a kasar. Ya ce, duk da tarin nasarorin da aka cimma a Saliyo, kasar na bukatar tallafin kasashen duniya, wajen dorewar kokarinta, na shawo kan kalubalen da yakin basasar shekarun 1990 ya haifar.

Har ila yau, jami'in ya ce, akwai bukatar baiwa yaki da fatara, da karancin guraben ayyukan yi tsakanin matasa goyon bayan da ya dace. Baya ga bukatar tabbatar da kiyaye doka da oda, da inganta yanayin siyasar kasar.

An dai kafa ofishin UNIPSIL ne a shekara ta 2008, domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a Saliyo, ana kuma fatan rufe ofishin a hukumce a karshen watan nan na Maris.

A wani cigaban kuma kakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana gamsuwa ga kokarin da majalissar ta yi, don gane da farfado da zaman lafiya a Saliyo, yana mai cewa, hakan ya zama wani darasi da za a iya koyi da shi a nan gaba. Wannan dai ra'ayi ya dace da na zauren kwamitin tsaron majalissar, wanda ya yi amanna da irin gudummawar da ofishin UNIPSIL ya bayar a fagen farfadowar kasar ta Saliyo. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China