Shugabannin biyu sun yi shawarwari, inda suka nuna yabo kan huldar dake tsakanin kasashen biyu, da tsara hadin gwiwarsu, da sanar da kaddamar da shawarwarin yin cikini cikin 'yanci a tsakaninsu, a kokarin sa kaimi ga zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsu.
Haka kuma, shugabannin biyu sun halarci bikin daddale shirin zurfafa dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu, tare da yarjeniyoyin hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, raya ayyukan more rayuwa, nazarin teku, al'adu, ilmi da dai sauransu.
Ban da wannan kuma, shugabannin biyu sun halarci bikin yaye kyallen bude cibiyar al'adun Sin dake kasar Sri Lanka da bikin nune-nunen littattafan kasar Sin na birnin Columbo na shekarar 2014, kana sun halarci bikin bude tashar samar da wutar lantarki ta hanyar kwal ta Puttalam, wadda Sin da Sri Lanka suka hada gwiwarsu wajen gina ta. (Zainab)