Ya kara da cewa, kasar Sin ta samar da babban taimako ga kasar Zambia a lokacin da take gina layin dogo daga Tanzania zuwa kasar ta Zambia, haka kuma, kasar Zambia ta tsaya tsayin daka wajen taimaka wa kasar Sin kan farfado da babban matsayinta a zauren MDD.
Ya ce, cikin shekaru 50 masu zuwa, kasar Zambia za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwar tsakanin kasashen biyu, kuma Zambia na nuna godiya matuka ga kasar Sin kan yadda take samar wa kasashen Afirka goyon baya bisa bukatunsu ba tare da gindaya wani sharadi ba. Bugu da kari, kasar Sin na da fasahohin zamani masu kyau, kana kasashen Afirka na da albarkatun kasa, shi ya sa, hadin gwiwar bangarorin biyu yake samun ci gaba tare da kuma cimma moriyar juna. (Maryam)