Sin ta nuna goyon baya ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta dake dacewa da babbar moriyar jama'ar Ukraine
Jiya 5 ga wata a Auckland dake kasar New Zealand, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya ba da amsa kan tambayoyin da suka shafiaka yi masa dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin Ukraine da dakarun dake gabashin kasar suka daddale da kuma batun dangantakar dake tsakanin Ukraine da Rasha.
Wang ya bayyana cewa, Sin ta yi marhabin da wannan ci gaba da aka samu tare da kuma bayyana fatanta na ganin cewa za a bi yarjejeniyar yadda ya kamata domin ta dace da babbar moriyar jama'ar Ukraine cikin dogon lokaci.(Fatima)