Jami'in ya bayyana cewa, jiragen saman soja biyu na dakarun sun kai hari kan wasu sansanonin dakarun Misrata dake goyon bayan kungiyar masu kishin addini a birnin Tripoli a wannan rana.
Amma bangaren sojan sama na kasar Libya ya bayyana cewa, jiragen saman soja na kasashen waje ne suka kai wannan hari.
Tawagar musamman ta MDD dake kasar Libya ta bayyana a ranar 18 ga wata cewa, ta tattauna da kasashen Faransa da Italiya a wannan rana, inda suka bayyana cewa, ba su shiga cikin harin da aka kai ba. (Zainab)