Wata sanarwar da tawagar ta UNSMIL ta fitar, ta kuma bayyana takaicinta kan yadda fada tsakanin sassan biyu ya tilasta wa fararen hula da dama barin gidajensu yayin da wasu kuma suka jikkata baya ga kayayyakin da aka lalata
Bugu da kari tawagar ta bukaci sassan da ke arangama da juna da su amsa kiran da kasashen duniya ke yi dangane da kokarin da tawagar ta UNSMIL ke yi na ganin an hanzarta tsagaita bude wuta tare da kawo karshen zubar da jini da dakatar da asarar dukiyoyin da ake yi, ta yadda za a hanzarta magance matsalar da ake fuskanta a halin yanzu.
Tun a ranar 13 ga watan Yuli ne kasar ta Libya ta fara fuskantar kazamin tashin hankali tsakanin kungiyoyi masu kishin Islama da ke dauke da makamai da mayakan da ke goyon ra'ayin sakulanci a kokarin da suke na kwace birnin Tripoli.(Ibrahim)