Kakakin sojojin ya kuma bayyana cewa, dakarun Ansar al-Sharia masu kishin addini sun kai hari ga sojojin musamman na kasar a wannan rana ne a kokarin da suke na kwace ikon mallakar filin jiragen sama na Benina dake birnin Benghazi.
Ya ce, wannan dauki ba dadi ya haddasa mutuwar sojoji 10 a wannan rana, yayin da wasu guda 10 suka ji rauni. Sai dai sojojin musamman na kasar ta Libya sun samu galaba a kan dakarun sakamakon taimakon da suka samu daga sojojin saman kasar. (Zainab)