in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan tawaye a Libya na zargin Masar da hadaddiyar daular Larabawa da kai farmaki cikin kasarsu
2014-08-24 16:56:41 cri
A jiya Asabar ne wani kakakin kungiyar mayakan sa kai na birnin Misratan kasar Libya, ya zargi kasar Masar da mahukuntan hadaddiyar daular Larabawa ta UAE da kaddamar da wasu hare-hare ta sama kan wasu sansanonin kungiyar a kusa da filin jirgin saman kasar dake birnin Tripoli.

Kaza lika a jiyan ne dai wannan kungiyar mayakan sa kai ta Misrata, ta sanar da kame ikon babban filin jirgin saman kasar dake birnin na Tripoli.

Tun dai a shekarar 2011 bayan kifar da tsohuwar gwamnatin shugaba Gadaffi, kungiyar mayakan Zintan ke rike da ikon filin jirgin saman na birnin Tripoli, kafin sanarwar sauyawar hakan da 'yan Misrata suka fitar, koda yake dai dakarun Zintan ba su tabbatar da gaskiyar hakan ba tukuna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China