Sai dai sabuwar majalisar dokokin kasar wato babban taron wakilan jama'ar kasar ta nuna rashin amince da wannan nadi, matakin da ya tabbatar da kasancewar majalisun dokoki biyu da firaministoci biyu a kasar.
A wani bangaren kuma karkashin shirin shiga tsakani na kasar Masar, ministocin harkokin wajen kasashen Libya, da Masar, da Tunisia, da Algeria, da Sudan, da kuma Chadi da ma wasu manyan jami'an kasar Nijar, sun gudanar da wani taro a birnin Alkahira game da batun warware rikicin kasar ta Libya, da kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar, inda ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoukry ya bayyana cewa, bayan shawarwarin da ministoci da manyan jami'ai mahalarta taron suka yi, sun amince da shawarar kasar Masar game da kokarin dawo da zaman lafiya a kasar Libya, ta hanyar kawar da makamai daga kungiyoyin fararen hular kasar.
Mr. Shoukry ya ce suna goyon bayan sabuwar majalisar dokokin kasar da aka zaba, da batun sake kafa hukumomin kasar da dai sauransu, kuma kasashen duniya ba za su tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ba.
Har ila yau an shawarta game da ayyukan yaki da ta'addanci, da kokarin cimma burin samun sulhu a kasar Libiya, da tsara sabon kundin mulkin kasar, tare da taimakawa gwamnatin kasar wajen gina tsarin sojojin kasa da dai sauransu. (Zainab)