Wata sanarwa da majalisar ta fitar a ranar 24 ga watan nan, ta bayyana yadda dakarun kungiyar Fajr Libya da na Ansar Al-Sharia suka kaddamar da hare-hare kan hukumomin gwamnatin kasar, tare da barnata ababen more rayuwar jama'a a biranen Tripoli da Benghazi.
Ci gaba da dauki ba dadi tsakanin sassan mayakan sa kai a kasar ta Libiya dai na da nasaba da gazawar da tsagin kungiyar 'yan kaifin kishin addini ya yi, na lashe zaben majalisar wakilan kasar a karshen watan Yunin da ya shude.
Kaza lika manazarta harkokin siyasar kasar na hasashen cewa, gwagwarmayar da masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ba-ruwanmu ke yi, game da damke ikon muhimman yankunan kasar ne ke dada tsananta fadace-fadace da ke faruwa a halin yanzu, matakin da kuma ke kara dagula yanayin da kasar ke ciki. (Zainab)