Mista Qin ya bayyana cewa, kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya aika da wata wasika zuwa ga takwaransa na majalisar wakilan kasar Birtaniya, saboda kwanan baya, kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan Birtaniya ya tambayi kasar Sin dangane da yadda take aiwatar da sanarwar hadin gwiwa ta kasashen Sin da Birtaniya.
Mista Qin ya tabbatar da cewa, kasashen Sin da Birtaniya sun tuntubi juna, inda Sin ta bayyana matsayinta a hukumance, lamarin da ya yi daidai kuma ya cancanta. (Tasallah)