Ana saran zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ya tattauna wannan bukata kafin ya kammala zamansa a ranar Lahadi.
Zhang Dejiang ya ce, daftarin da yankin na Hong Kong ya gabatar yana son ya fara aiki ne a zaben jami'in farko na yankin na musamman da za a yi a shekarar 2017 da kuma zaben 'yan majalisa a shekara ta 2016.
Yanzu dai mambobin majalisar wakilan jama'a sun nazarci rahoton da jami'in farko na yankin Hong Kong na musamman ya gabatar game da gyaran fuska a harkokin zaben, ko da ya ke ba a yi wani karin haske game da sauran abubuwan da ke kunshe cikin daftarin ba.
A shekara ta 2012 ne kwamitin majalisar wakilan jama'a ya zabi jami'in farko na yankin na Hong Kong na yanzu, yayin da yanzu kuma yankin ke nemen a baiwa al'ummar yankin damar zaben shugabanninsu da kansu a zaben shekarar 2017. (Ibrahim Yaya)