Mr. Song wanda ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da shugabar ofishin kansula na kasar Burtaniya dake yankin na Hong Kong Caroline Elizabeth Wilson, ya yi fatan kasar Burtaniya za ta mai da hankali kan kiyaye dangantakar dake tsakaninta da Sin, ta kuma yi kokarin kiyaye yanayin zaman karko da wadatar yankin.
Har ila yau wata sanarwa daga shafin yanar gizon ofishin babban jami'an musamman da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin ta aike zuwa yankin na Hong Kong, ta ce, ganawar da Mr. Song ya yi da Wilson a ranar 29 ga watan Mayu, ta karkata ne ga shawarta batutuwa da suka shafi dangantakar kasashen biyu, da yanayin siyasa, da tattalin arzikin yankin na Hong Kong.
Kaza lika Mr. Song ya jaddada matsayin gwamnatin kasar Sin, dangane da ka'idojin bunkasa harkokin yankin na Hong Kong. (Maryam)