Mr. Zhang ya bayyana hakan ne dai ya yin bikin rufewar taro karo na 10 na zaunannen kwamitin karo na 12. Kaza lika da yammacin wannan rana, an zartas da kudurorin da suka shafi harkokin zaben shugaba mai kula da harkokin yankin musamman na Hong Kong, da kuma yadda za a iya kai ga kafa majalisar dokoki a yankin a shekarar 2016, a taron zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa ta Sin.
Bugu da kari, Zhang Dejiang ya ce, goyon bayan yankin musamman na Hong Kong bisa kudurin neman bunkasuwarsa karkashin babbar dokar kasa ya dace da tsarin dimokuradiyyar yankin, kuma hakan ne matsayin da gwamantin kasar Sin ke kai a ko da yaushe. (Maryam)