Kantoman yankin musamman na Hongkong Leung Chunying ya bayyana a yammacin ranar 31 ga watan Agusta cewa, jami'an da ke kula da harkokin yankin da membobin majalisar da ba jami'ai ba sun nuna goyon baya ga kudurin da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yanke.
Yanzu kantoman da gwamnatin yankinsa za su yi kokarin aiwatar da kudurin don cimma burin zaben babban jami'in yankin na musamman wanda jama'a fiye da miliyan 5 za su zaba.
Bangaren 'yan kasuwa shi ma ya yi maraba da wannan kuduri.
Shugaban babbar kungiyar 'yan kasuwa ta yankin Hongkong YK Pang ya bayyana cewa, zaben wanda zai shugabanci harkokin yankin na Hong Kong shi ne burin jama'ar yankin a zaben da za a yi a shekarar 2017 don zaben babban jami'in yankin na musamman dake dacewa da ra'ayoyin jama'ar yankin, wannan zai kasance abu mai muhimanci a tarihin yankin.(Zainab)