Ranar 29 ga wata, kwamitin yaki da wariyar al'umma na MDD ya gabatar da wata shawara kan rahoton da kasar Japan ta mika masa a lokaci-lokaci game da yadda take aiwatar da "yarjejeniyar kasa da kasa ta yaki da wariyar al'umma", inda ya mai da hankali sosai saboda babu dokar musamman ta yaki da wariyar al'umma a Japan, kuma ana ci gaba da nuna wariyar al'umma a wannan kasa.
Bayan haka kuma, Madam Anastasia Crickley, mataimakiyar shugaban kwamitin ta bayyana a yayin taron manema labaru cewa, matan da aka tilastawa yin karuwanci ga sojojin Japan a lokacin yakin duniya na biyu ba a kiyaye hakkokinsu ba, sai dai a bar shari'a ta yi aiki, tare da ba su diyya yadda ya kamata. Kwamitin ya bukaci Japan da ta nemi gafara cikin sahihanci daga matan da aka tilastawa yin karuwanci ga sojojin Japan da kuma iyalansu, tare da ba su isasshiyar diyya. Kwamitin ya kuma yi tir da dukkan yunkurin da aka yi na shafa wa matan kashin kaji ko musunta tilasta musu yin karuwanci ga sojojin Japan.(Tasallah)