Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wannan kuduri ne yayin taron da ya gudanar game da yadda za a magance rikice-rikice. Kudurin ya tanadi cewa, magance rikice-rikice yana daya daga cikin ayyukan kwamitin sulhun na kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, kana aiki ne da kasa da kasa suka daukar nauyin gudanar wa.
Kamata ya yi MDD ta yi la'akari da rawar da gwamnatocin kasa da kasa suke takawa yayin da take daukar matakan magance rikice-rikice.
A gun taron, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya yi jawabi cewa, tilas ne a zabi hanyar magance rikice-rikice mai dorewa, tare da maida hankali kan halin da ake ciki kafin daukar duk wasu matakai. Ya ce, ya kamata a mai da kundin tsarin MDD a matsayin tushen aikin magance rikice-rikice, wanda ya bukaci kasashe membobin MDD su dauki alhakin magance rikice-rikice da ke damunsu, sa'an nan kuma ya kamata dukkan ayyukan magance rikice-rikice da kasa da kasa da kuma MDD suka yi su dace da kundin tsarin MDD, da girmama 'yancin mallakar kasashe, bisa makasudin mara baya ga kokarin da kasashe ke yi da kuma neman goyon baya da yin hadin gwiwa tare da kasashen. (Zainab)