in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD 43 a zirin Golan
2014-08-29 10:56:03 cri

MDD ta tabbatar a ranar alhamis 28 ga wata cewa, Dakaru masu dauke da makamai sun kama ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD guda 43 a zirin Golan a wannan rana. A game da hakan babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon da kwamitin sulhu na MDD sun soki wannan lamarin, tare da nuna bukatar sako wadannan ma'aikata ba tare da sharadi.

Bisa labarin da muka samu, an ce, a safiyar ranar ta alhamis wadannan dakaru suka kame ma'aikatan kiyaye zaman lafiya guda 43 'yan asalin kasar Fiji wadanda suka jibge a sansanin da ke kudancin yankin kariyar soja a zirin Golan, ban da wannan kuma, dakarun sun kayyade aikin ma'aikatan kiyaye zaman lafiya guda 81 'yan asalin kasar Philippines da ke jibge a wasu sansanoni biyu.

Bisa kididdigar da MDD ta bayar an ce, rundunar sa ido ta musamman ta MDD wato UNFOD na kunshe da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya 1223 da suka zo daga kasashe 6 wato Fiji, da India, da Ireland, da Nepal, da Holland, da kuma Philippiens. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China