in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana zaburar da kaimi domin ganin ta cimma manufarta ta MDGs
2014-08-19 14:54:11 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya kebe wasu kwanaki 500, na gudanar da aiki tukuru domin cimma manufarta ta MDGs, wadda dukkan mambobin majalisar suka tsara a shekarar 2000 dangane da harkokin bunkasuwa.

Ban Ki-moon ya ce, aikin zai ceto rayuwar jama'a tare da gina ginshiki mai karfi na samar da ci-gaba mai dorewa bayan shekara ta 2015, kuma wannan aiki zai taimaka wajen jagorantar samar da wani yanayi na zaman lafiya tare da baiwa dan Adam darajarsa.

Babban sakataren na majalisar ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen zaburar da kaimi, domin cimma manufarta ta MDGs kafin karshen shekara ta 2015.

Ban Ki-moon ya ce, taswirar da aka tsara domin cimma manufar ta MDGs ta samu nasara, inda aka rage matsalar talauci da kusan rabi, kuma yanzu yara mata da yawa suna zuwa makaranta, kana kuma iyaye mata suna rayuwa a yayin da suka zo haihuwa, har wa yau kuma an samu nasara wajen tunkarar yaki da cututtukan zazzabin Malaria, da tarin fuka, da sauran cututtuka masu kashe bil'Adama. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China