Ms Maria do Valle Ribeiro dai za ta maye gurbin Mr Gana Fofang ne daga kasar Kamaru wanda yake wannan mukamin tun a watan Fabrairun shekara ta 2011, in ji sanarwar wadda ta yi bayanin cewa Babban magatakardar tuni ya mika godiyar sa ga Mr Fofang bisa ga hazaka da juriya da ya nuna a lokacin aikin sa a kasar ta Guinea Bissau.
A cewar wannan sanarwa Ms Do Valle Ribeiro tana da kwarewa a bangaren ayyukan cigaba da jin kai na tsawon shekaru 25 inda ta rike manyan mukamai a majalissar da kuma wassu kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen duniya a Afrika, Asiya da Caribbean.
Yanzu haka ita ce babbar jami'a ta majalissar, kuma wakiliyar UNDP a kasar Angola. Kafin wannan mukamin nata ta rike manyan mukamai a asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF, da babbar jami'a ta MDD, kuma wakiliyar UNDP a kasar Mauritaniya a tsakanin 2008 -2010.
An dai haifi Ms Maria do Valle Ribeiro ne a Portugal a shekara ta 1957, tana da takardar digiri na biyu a bangaren kimiyyar cigaban tattalin arziki da tsare tsare daga jami'ar Wales. (Fatimah)