in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mashirya gasar Olympic ta birnin Nanjing sun cancanci yabo, in ji shugaban IOC
2014-08-25 10:04:34 cri

Yayin da ya rage 'yan kwanaki kadan a kammala gasar wasannin Olympic ta matasa dake gudana a birnin Nanjing na nan kasar Sin, masu fashin baki na ci gaba da jinjinawa mashirya gasar, bisa tarin nasarorin da aka cimma.

Da yake tsokaci game da yadda wasannin na Olympic na wannan karo ke wakana, shugaban kwamitin Olympic na kasa da kasa IOC Thomas Bach, ya ce, mashirya gasar sun cancanci yabo bisa kokarinsu na shirya gasar da ta yi matukar samun karbuwa yadda ya kamata.

Bach ya ce, ya gamsu da ganin yadda matasa ke fafatawa a wannan gasa, wadda ta kasance ta biyu da Sin ke daukar nauyin gudanarwa. Hakan a cewar sa, ya shaida cikakkiyar kwarewa da mashirya gasar suka nuna. Ciki hadda batun hada tsarin gudanar kyakkyawar alaka tsakanin mahalarta gasar da kuma nagarcin tsarin gudanarwa.

Har wa yau Bach ya bayyana farin cikinsa, game da yadda aka kyautata amfani da kayayyakin wasan Olympic da ya gabata a shekarar 2008 a gasar birnin na Beijing, yana mai cewa, hakan abin alfahari ne gare shi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China