in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su tinkari kalubalen da sauyin yanaki ke haifarwa harkar lafiya
2014-08-28 16:39:37 cri

Sakamakon bincike da dama na nuni ga irin tasirin da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar jikin bil'adama. Wannan ne ma ya sanya a ranar 27 ga watan nan aka kira taron kasashen duniya da aka yiwa lakabi da "lafiyar jiki da yanayi". Taron dai wanda aka bude a birnin Geneva, ya bada damar tattaunawa kan matakan da kasashen duniya ya dace su dauka wajen tinkarar kalubale da sauyin yanaki ke haifarwa lafiyar jikin dan Adam.

Mahalartan taron sun kunshi wasu shugabannin hukumomin MDD, da ministocin kiwon lafiya da na muhalli na kasashen duniya da dama, da ma wasu kwararru a fannonin kula da yanayi. Sauran mahalartan sun hada da masana a fannin samun bunkasuwa mai dorewa, da wakilan kungiyoyin jama'a, wadanda yawansu ya wuce 300.

Za a shafe kwanaki uku ana taron, inda za tattauna kan manyan al'amura biyu, na farko, inganta kwarewar hukumomin kiwon lafiya, domin tinkarar kalubale da sauyin yanaki ke haifarwa lafiyar jiki. Abu na biyu, shi ne rage dalilan da ke haifar da sauyin yanayi, da kara karfafa lafiyar jikin bil'adama. Game da hakan babbar darekatar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Madam Margaret Chan, ta yi nuni cewa, shaidu masu yawan gaske sun nuna cewa, sauyin yanayi yana kawo babbar barazana ga lafiyar jama'a. Ta ce,

"Yanayi na da tasiri ga iskar da jama'a ke shaka, da abinci da ruwa da muke sha. Shaidu masu yawan gaske sun bayyana cewa, ayyukan 'yan Adam na kara haifar da illa ga muhalli, wanda hakan ke kara sanya mu damuwa, ana kara samun sabon matsayi na barkewar mugun yanayi, kuma duniya tana samun raguwa wajen kwarewarta ga kiyaye rayuwar 'yan Adam yadda ya kamata."

Hukumar WHO ta yi nuni da cewa, ko da yake mai yiyuwa ne dumamar yanayi ya samar da wata moriya 'yar kadan a wasu yankuna, kamar rage mutuwar halittu a lokacin sanyi, da kara yawan hatsin da ake samu, koda yake a hannu guda sauyin yanayin na haifar da mugun tasiri ga lafiyar jama'a. Hakika dai sauyin yanayi ya kawo illa ga al'ummomi, da muhalli, da ke da nasaba da lafiyar jikin jama'a, kamar iska mai tsabta, da ruwan sha mai inganci, da isasshen abinci da wuraren kwana masu inganci ga halittu.

Idan aka leka sassan duniya, ana iya ganin yadda daga shekarun 1960 ya zuwa yanzu, yawan bala'un da halittu ke haduwa da su masu nasaba da yanayi ya ninka har sau 3, wadanda kuma suka haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 60 a kowace shekara, yawancinsu kuma sun faru ne a kasashe masu tasowa. Wani kwararre daga ofishin kula da harkokin lafiyar jikin jama'a da muhalli a hukumar WHO Mista Diarmid Campbell-Lendrum ya bayyana cewa,

"Kamar yadda muka sani, iska mai zafi tana iya kashe mutane, wannan batu ne da aka amince da shi a shekarar 2013 a Turai. Zai kuma tsallaka ga tsakiyar karnin da muke ciki, mai yiyuwa ne karuwar aukuwar iska mai zafi za ta dadu a nan gaba, wato a yanzu irin yanayi na aukuwa kamar karo daya a ko wadanne shekaru 20, amma a nan gaba adadin zai karu zuwa daya a ko wadanne shekaru 5."

Amma idan an iya daukar matakai masu amfani, za a iya rage wannan mummunar illa. Ga misali, ta hanyar canza manufofin makamashi, da jigilarsu, zasu iya rage yawan iskar da ke dumama yanayi, da kuma rage gurbacewar iska, wanda hakan ka iya ceton miliyoyin jama'a. Game da hakan darektar ofishin kula da harkokin lafiyar jikin jama'a da muhalli na hukumar WHO Madam Maria Neira ta bayyana cewa,

"Mun zo ne daga ofishin da ke kula da lafiyar jikin jama'a, mun kuma yi matukar fahimtar cewa, idan muka dauki matakai na rage fitar iska mai dumama yanayi, hakan na iya rage gurbatar iska, wanda hakan zai iya samar da babbar moriya ta fannin inganta lafiyar jikin bil'adama."

A gun bikin bude taron na wannan rana, ofishin da ke kula da harkokin yara na hukumar WHO ya nuna burin yara game da wannan taro.

"A madadin yara da ke zaune a wannan kyakkyawar duniya, mun gabatar da wannan takarda mai kunshe da burinmu, domin mun lura da tasirin sauyin yanayi da lafiyar jiki, kuma mun lura da makomar duniya a nan gaba." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China