An bude taron kiwon lafiya na duniya karo na 67 a ranar litinin 19 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland, Shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin darektan kwamitin da ke kula da kiwon lafiya da tsara shirin haihuwa na kasar Mista Wang Guoqiang ya yi wani jawabi a wajen taron, inda ya gabatar da ra'ayin kasar kan dangankatar da ke tsakanin sauyin yanayi da lafiyar 'dan Adam.
Wang ya yi nuni da cewa, sauyin yanayi ya zama wani babban kalubale ga lafiyar 'dan Adam a karni na 21, gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna mai da hankali sosai kan babbar illa da sauyin yanayi ke kawo ma lafiyar 'dan Adam da zamantakewar al'umma da tattalin arziki. Ya ce don haka kasar Sin ta dauki wasu matakai a jere don tinkarar hakan.
A shekara ta 2007, gwamnatin kasar Sin ta tsara shirin daukar matakai kan kare muhalli da lafiyar jama'a, a shekara ta 2013, Sin fitar da manyan tsare-tsare na tinkarar sauyin yanayi, inda aka tabbatar da kafa wani tsari na sa ido kan mummunar yanayi da lafiyar jama'a, da gudanar da hidima wajen nazari kan hadarin da sauyin yanayin zai bayar ga lafiya da bayar da bayanai, da kimantawa illoli ga lafiyar jama'a daga tsananin zafi, da ambaliyar ruwa, da fari da dai sauran mawuyacin yanayi, da yin gargadi da tinkara cikin gaggawa.
Mr Wang sai ya jaddada cewa, kasar Sin tana fuskantar wani hali mai tsanani wajen magance illa ga lafiyar jama'a daga sauyin yanayi, sabo da haka ne take son yin kokari tare da sauran kasashe don tinkarar kalubale tare. (Danladi)