in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yabawa kasashen BRICS da yaki da dumamar yanayi
2014-05-05 13:24:13 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yaba da hobbasa din da kasashen BRICS masu saurin samun cigaban tattalin arziki suke yi, musamman gumuzun da suke yi na dakile matsalar dumamar yanayi.

Babban sakatare na MDD ya bukaci kasashen da su kara zage damtse a gudumuwar da suke bayarwa wajen yaki da dumamar yanayi.

Ban Ki-moon ya ce, gudumuwar da kasashen BRICS wato Brazil da Rasha da India da Sin da Africa ta Kudu ke bayarwa a wajen magance matsalar dumamar yanayi, wani abu ne mai mahimmancin gaske, saboda kasashen na kan hanyarsu ta rikidewa zuwa kasashen da suka ci gaba.

Babban sakataren MDD ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani taron manema labarai a Abu Dhabi a wani taro wanda ke share fagen babban taron koli a kan yanayi wanda za'a yi a birnin New York a watan Satumba mai zuwa.

A taron na Abu Dhabi, akalla wakilai kimanin 1000 wadanda suka hada da ma'aikatun gwamnatoci da kuma kwararru a kan makamashi suka sami halartar taron. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China