A Jiya Asabar ne wasu bama-bamai da aka dana cikin wasu motocin suka fashe a garin Hull Muller na gabashin kasar Lebanon dake kusa da yankin iyakar kasar Syria, wanda ya haddasa a kalla mutuwar mutane guda 4, yayin da mutane sama da 20 suka jikkata.
Sanarwar da kwamitin sulhu na MDD ya bayar, ta yi kira ga dukkan 'yan kasar da su hada kai wajen yaki da dukkan ayyukan da za su lalata zaman karko na kasar, ta kuma jaddada muhimmancin kiyaye manufar rashin tsoma baki a rikicin Syria.
Bugu da kari, Mr. Ban Ki-moon ya kuma ba da sanarwa ta hannun kakakinsa, inda ya yi kira ga jama'ar kasar Lebanon da su nuna goyon baya ga hukumomin gwamnatin kasar da suka hada da rundunar sojan kasa da kuma sojojin tsaron kasa, wannan ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen kiyaye tsaro da zaman karko na wannan kasa. (Maryam)