Game da wani ra'ayin kasar Sin ganin yanzu an riga an gabatar da sakamakon babban zaben, inda shugaba Mugabe ya yi nasara, Mr Hong Lei ya ce bisa sakamakon da kwamitin zaben kasar Zimbabwe ya gabatar a kwanan baya, ya nuna cewa shugaba Mugabe da jam'iyyar ZANU-PF dake karkashin jagorancinsa sun lashe babban zaben. Don haka Sin take taya kasar murna game da hakan.
Ban da haka, Hong ya yi bayanin cewa, a matsayin aminiyar Zimbabwe, Sin tana fatan Zimbabwe za ta kara samun ci gaba bisa wannan babban zabe, kuma Sin za ta ba da goyon baya ga kokarin Zimbabwe na tabbatar da zaman lafiya da neman samun ci gaba.(Fatima)