in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiwatar da atisayen soja na kungiyar hadin kai ta Shanghai
2014-08-25 15:30:12 cri

An gudanar da bikin fara atisayen soja na kungiyar hadin kai ta Shanghai mai lakabin "aikin shimfida zaman lafiya na shekarar 2014" a ranar 24 ga wata a jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin, wannan ya bayyana cewa, a hukunce aka fara aiwatar da atisayen soja na kungiyar hadin kai ta Shanghai.

Bisa labarin da aka samu, an ce, sojojin da yawansu ya wuce dubu 7 daga kasashen Kazakhstan, da Sin, da Kyrgyzstan, da Rasha, da kuma Tajikistan sun shiga atisayen soja na wannan karo, wadanda suka kunshe da sojojin kasa, da sojojin sama, da sojoji masu ayyuka na musamman da dai sassan sojojin da ke gudanar da aikin bincike da sa ido, da safiyo, da dudduba yanayin sama da na ruwa, da dai sauransu.

Mataimakin kwamanda mai kula da sashen ba da jagoranci ga atisayen kuma mataimakin kwamandan sojojin Rasha rukuni na 29 Mikhail Yakovlevich Nosulev, ya nuna cewa, a halin yanzu dai ta'addanci yana faruwa a duk fadin duniya baki daya, don haka yaki da ta'addanci ya zama wani nauyi da ya hau kan wuyan ko wane bangare. Ya yi bayanin cewa, makasudin gudanar da atisayen soja na wannan karo shi ne, domin yaki da ta'addanci, da inganta kwarewar sojoji wajen tsaron kasa. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China