in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzania za ta gina cibiyar cinikayya ta kayayyakin Sin
2014-08-21 10:45:28 cri

Hukumomin Tanzania sun ce, nan ba da dadewa ba ne za'a fara gina wata cibiyar cinikayyar hadin gwiwa tsakanin Tanzania da kasar Sin, wacce za ta samar da kayayyaki masu aminci daga kasar Sin domin kasuwannin gabashi da tsakiyar Afrika.

Ministan masana'antu da cinikayya na Tanzania, Abdallah Kigoda ya ce, kasar Sin ita ce za ta dauki nauyin gina cibiyar a kan kudi har dalar Amurka miliyan 412.5.

A nata bangare, gwamnatin Tanzania ta fitar da kudi kimanin dalar Amurka miliyan 33 domin biyan diyya filayen jama'a kusan 1,020, wadanda ginin wannan cibiya zai shafa a garin Kurasini, babban birnin Dar-es Salam na hada-hadar kasuwanci.

Wannan gamayyar ta biyo bayan taron hadin gwiwa a shekarar 2009, tsakanin Afrika da kasar Sin, kuma cibiyar za ta kai fadin murabba'in hekta 60.4 a garin Kurasini, kuma ginin zai hada da yankunan shimo la Udongo, Mivinjeni da kiungani.

Mataimakiyar ministan masana'antu da cinikayya Janet Mbene, ta ce, ayyukan za su samar da guraben ayyukan yi kimanin dubu 25 kai tsaye, ga 'yan kasar ta Tanzania, da kuma wasu karin ayyukan wadanda ba na kai tsaye ba kimanin dubu dari, tare da kara samar da haraji ga gwamnati. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China