Ministan albarkatun kasa da yawon shakatawa na kasar Tanzaniya Lazaro Nyalandu ya bayyana cewa, an samu karuwar wasu nau'in giwaye da ke gandun dajin Serengeti-Maasi Mara daga 258 a shekarar 1986 zuwa 7,535 a yanzu. Wani kidaya na baya-bayan nan da wasu masana kimiyya daga kasashen Tanzaniya da Kenya suka gudanar wadanda suka hada muhallin halittu guda da ya kai murabbin sq kilomita 32,000 na yankin Ngorongoro, dajin shakatawa na Serengeti, gundumar Maswa, Ikongoro da yankunan kula da namun daji na Grumeti da gandun dajin Kijereshi a bangaren Tanzaniya da kuma dajin yawon shakatawa na Masai Mara da ke daura da yankin Narok a Kenya.
Bugu a kari a yayin kidayar, an gano bauna kimanin 61,896, adadin da ya nuna cewa, an samu karuwar kashi 18 cikin 100 na yawan bauna 54,974 da ake da su a shekarar 1986. (Ibrahim)