in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon firaminista a Mauritania
2014-08-21 10:18:27 cri

An nada Yahya Ould Hademine a matsayin sabon firaministan kasar Mauritania a ranar Laraba, domin maye gurbin Dokta Moulaye Ould Mohamed Laghdaf, wanda ya gabatar da takardar murabus dinsa a wannan rana, in ji wata majiya mai tushe. Wani na hannun daman shugaban kasar Mauritania Ould Abdel Aziz, mista Hademine ya rike mukamin ministan sufuri da gine-gine a shekarar 2009. A wannan ma'aikata, mista Hademine, injiniyan da ya samu horo a kasar Canada, ya jagoranci manyan gine-ginen hanyoyi, tashoshin jiragen ruwa da na jiragen sama a kasarsa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China