in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar adawa a Zimbabwe na takaddama kan batun tsige Morgan Tsvangirai
2014-04-28 10:15:21 cri
Kakakin jam'iyyar adawa ta MDC-T a kasar Zimbabwe, mista Douglas Mwonzora ya yi fatali a ranar Lahadi da matakin sakatare janar na jam'iyyar Tendai Biti ya gabatar na dakatar da shugaban jam'iyyar Morgan Tsvangirai.

A yayin wani zaman taron jam'iyyar MDC-T da aka kira a ranar Asabar da ta gabata, mista Biti ya sanar da dakatar da mista Tsvangirai, mataimakinsa Thokozani Khupe da ma wasu manyan kusoshin jam'iyyar, da ake zaginsu da take dokokin jam'iyyar wajen warware rikicin cikin gida na jam'iyyar.

Mista Mwonzora, dake bayani gaban manema labarai, ya nuna cewa matakin dakadar da Tsvangirai ba ya da tushe ko kadan, domin mista Biti ba ya da wani hurumin daukar irin wannan mataki tare kuma da jaddada cewa 'yawan adadin mambobi bai cika a yayin da mista Biti ya kira wannan taro. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China