Da yake karin haske game da wannan batu, yayin wani taron karawa juna sani da ya gudana a birnin Harare, shugaban hukumar ta ZIMRA Jamar Gershom Pasi, ya ce daukar wannan mataki zai horewa masu matsakaita, da kananan sana'oi damar biyan haraji bisa radin kan su kuma cikin sauki. Baya ga kasancewar hakan wani mataki da zai magance rashin kyakkyawan tsarin tattara harajin a sassan da ba na gwamnati ba.
Tabarbarewar yanayin tattalin arzikin da Zimbabwe ke fuskanta tun daga karshen shekarun 1990 kawo yanzu dai, ya taka muhimmiyar rawa wajen gurgunta mafiya yawan manya da matsakaitan kamfanonin kasar, matakin da kuma ya haifar da karuwar kananan harkokin cinikayya, da a mafiya yawan lokuta ke kaucewa biyan haraji ko ta'ammali da bankuna.(Saminu)