'Yan majalisar wakilai na kasar ta Libya kimanin 141, suka kada kuri'a na amincewa da zaben shugaban kasar a nan gaba a karkashin wani tsari da zai baiwa jama'a damar zaben shugaban kasar su kai tsaye
Kamar dai yadda tsarin maida mulki na kasar Libya ya tanada, sabuwar majalisar dokokin kasar, wato majalisar wakilai ta kasar ta maye gurbin tsohuwar babbar majalisar rikon kwarya ta kasar, kuma nan gaba kadan za'a gudanar da zaben shugaban kasa, domin kawo karshen matakan mika mulki na kasar
Kawo ya zuwa yanzu, majalisar wakilan kasar bata kebe wata ranar ba domin gudanar da zaben shugaban kasar
Kasar Libya ta fuskanci karin tashe-tashen hankula tun bayan rikicin shekarar 2011, wanda ya kifar da gwamnatain tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.,
Tashe-tashen hankulan da aka yi a baya-bayan nan a tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda ke gaba da juna, a manyan garuruwa da suka hada da Tripoli da Benghazi na daga cikin abubuwan da ake fargabar zai iya jefa kasar cikin yakin basasa. (suwaiba)