A cewar kakakin ofishin, lokaci ya yi da daukacin sassan da basa ga maciji da juna za su koma teburin shawara, karkashin shirin UNSMIL na shiga tsakani.
Kaza lika ofishin tawagar ta wanzar da zaman lafiya ya yi kira ga bangarorin dake adawa da juna, da su kauracewa amfani da karfi wajen warware banbancin ra'ayin siyasa dake tsakanin su.
Kakakin ofishin ya kuma bayyana damuwa kwarai, game da halin karacin kayayyakin kula da lafiya da ake fuskanta, da lalacewar ababen more rayuwa, tare da matsalar rasa matsuguni da dubban al'ummar kasar ke fuskanta.
Kaza lika ya bayyana damuwar ofishin sa, game da ci gaban rikici a sassan gabashin kasar, tare da hare-haren da ake kaiwa kan ofisoshin 'yan sanda da na soji, da ma amfani da jiragen saman yaki wajen kaddamar da irin wadannan hare-hare.