Rahotanni sun bayyana cewa, an taras da gawar jami'in wanda ke jagorantar cibiyar tsaron kasar birnin ne da yammacin ranar Talata, a gabashin birnin na Tripoli cikin motar sa dauke da harbin bindiga da dama.
Wannan ne dai karo na biyu kasa da wata guda, da aka hallaka wani babban jami'i a kasar ta Libiya, inda a 'yan kwanakin baya ma wasu maharani suka harbe kanar Hassan Kamuka, jami'in dake jagorantar hukumar tsaron birnin Sabratha.
Kasar Libiya dai na shan fama da tashe-tashen hankula, tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Ghaddafi a shekarar 2011, inda kuma ake tsoron dauki ba dadin da dakaru masu dauke da makamai ke yi yanzu haka a kasar, na iya rikidewa zuwa yakin basasa.